Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - zuwa Aljanna, sai ya ce: ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta sai ya dawo, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa wani daya ba zai ji ta ba sai ya shigeta.
Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan ki, sai Ya ce; Tafi zuwa gareta ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga ta an kewayeta da abubuwan ki, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa shiga cikinta .
Ya ce: Tafi ka yi duba zuwaga wuta da kuma abinda na tanada ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga shashininta yana hawa kan sashi, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa ba wanda zai shigeta.
Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan sha'awa , sai ya ce; ka koma ka yi duba zuwa gareta, sai ya yi duba zuwa gareta sai ga shi ita kuma an kewayeta da abubuwan sha’awa, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa tsira daga gareta a ce bai shigeta".
Explanation
Benefits
Wajabcin yin imani da abinda ke boye da kuma dukkanin abinda ya zo daga Allah da manzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Muhimmancin hakuri akan abubuwan ki; domin su ne hanya masu kaiwa zuwa ga Aljanna.
Muhimmancin nisantar abubuwan da aka haramta; domin su ne hanya mai kaiwa zuwa ga wuta.
Sanya Aljanna abar kewayewa da abubuwan ki, wuta kuma da sha'awowi, shi ne ke hukunta jarraba a rayuwar duniya.
Hanyar Aljanna mai wahala ce, kuma tana bukatuwa zuwa ga hakuri da fama tare da imani, hanyar wuta kuma abin cikawa ce da abubuwan jin dadi da sha'awowwi a anan duniya.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

