Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki, sai mai kira ya yi kira: Yaku 'yan Aljanna, sai su dago kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, dukkaninsu kuma sun ganta, sannan ya yi kira: Yaku 'yan wuta, sai su miko kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu sun ganta, sai a yankata sannan ya ce: Ya ku 'yan Aljanna dawwama babu mutuwa, ya ku 'yan wuta dawwama babu mutuwa, sannan ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadin ranar nadama yayin da aka hukunta al'amari alhali su suna cikin rafkana} [Maryam: 39], wadannan suna cikin rafkanannun mutane a duniya {Su ba su Imani ba} [Maryam: 39]".
Explanation
Benefits
Gargadi mai tsanani daga tsoron Alkiyama kuma cewa ita ce ranar da na sani.
Bayanin dawwamar farin cikin 'yan Aljanna, da kuma dawwamar bakin cikin 'yan wuta.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

