na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Lallai ya kasance yana yin kabbara a kowacce sallar farilla da watanta, a Ramadan da waninsa, sai ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake yin ruku'u, sannan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode ma…

