na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Lallai ya kasance yana yin kabbara a kowacce sallar farilla da watanta, a Ramadan da waninsa, sai ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake yin ruku'u, sannan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan ya ce: Ya Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa kafin ya yi sujjada, sannan ya ce: Allah ne mafi girma a yayin da yake tafiya ƙasa don yin sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa daga zama a raka'a ta biyu, zai aikata haka a kowacce raka'a, har sai ya gama sallar, sannan ya ce a yayin da yake juyawa: na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya.
Explanation
Sannan Abu Huraira yake cewa a yayin da ya idar da sallar: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lallai ni ne mafi kusancinku kamaceceniya da sallar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce siffar sallarsa har ya bar duniya.
Benefits
Kwaɗayin sahabbai a kan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kiyaye sunnarsa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

