”
#5473HadeethEnc[Isnadinsa ingantacce ne]
Daga Abu Musa al-Ash'ari - yardar Allah ta tabbata a gare shi - idan ya ji tsoron mutane, sai ya ce: "Ya Allah, mun sanya ka a cikin kankan da kai, kuma muna neman tsarinka daga sharrinsu."
”
#5474HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce: "Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma".
”
#5475HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Samura ɗan Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gagreshi - ya ce: "Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne ma…
”
#5476HadeethEnc[Hasan ne kuma Ingantacce]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u", kuma an tambayeshi game da mafi yawan abin d…
”
#5477HadeethEnc[Ingantacce ne a baki dayan Riwayoyin sa]
Daga Abu Sa`id al-Khudri, yardar Allah ta tabbata a gare shi, wanda ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Ragowar na kirki ne, babu wani Allah sai Allah, tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Allah ya fi girma, kuma Allah ya fi girma”
”
#5478HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ji wani mutum yana yi wa ɗan uwansa wa'azi game da kunya, sai ya ce: "Kunya tana daga imani".
”
#5479HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama".
”
#5482HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa: ’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin bayan al’amari na, kuma Ka gyara mini duniya ta wacce na ke rayuwa a cikinta, Ka…
”
#5483HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana addu'a da wannan addu'ar. "Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena da wautata, da wuce gona da irina a cikin dukkan al'amarina, da abinda Kaine Maf…
”
#5485HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana barin waɗannan addu'o'i ba lokacin da ya yi yammaci ko ya wayi gari: "Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira, ya Allah lallai ni ina ro…
”
#5487HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga (Nana) A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koya mata wannan addu'ar: "Ya Allah ina roƙon Ka dukkan alheri, magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sa…
”
#5488HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ya kasance daga addu'ar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".