”
#5361HadeethEnc[Hasan ne ta wani Sanadin]
A kan Abdullah bin Amr - Allah ya yarda da su duka - a kan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Yardar Allah tana cikin gamsuwa ta iyaye, da fushin Allah a cikin fushin iyaye."
”
#5364HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kada ku zagi matattu; domin cewa sun iso zuwa abin da suka gabatar".
”
#5365HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (s…
”
#5367HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Jubair ɗan Mut'im - Allah Ya yarda da shi - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa; "Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba"
”
#5368HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa; "Annamimi ba zai shiga aljanna ba".
”
#5369HadeethEnc[Ingantacce ne]
A kan Abu Hurairah, Allah ya yarda da shi, a kan annabi, salati da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda ya ce: "Babu ɗayanku da zai yi tafiya a cikin tafin kafa ɗaya, ya ɗora su a kan dukkansu, ko ya tube su duka."
”
#5370HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai".
”
#5371HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Darda - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu wani abu mafi nauyi a ma'aunin mumini a ranar Alkiyama daga kyawawan dabi'u, lallai Allah Yana kin mai alfasha mai mummunar magana".
”
#5372HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to, ya sadar da zumuncinsa".
”
#5373HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullah bn Amr bin Al-Aas - Allah ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Daya daga cikin manyan zunubai shi ne mutum ya zagi iyayensa." Aka ce: Shin mutumin yana zagin iyayensa ne? Sai ya ce: Ee, ya zagi mahaifi…
”
#5374HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi dan Abbas - Allah ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: “Duk wanda ya ji hadisin wasu mutane alhali suna kiyayya da shi; Zuba a kunnuwansa yanzu a ranar sakamako ».
”
#5377HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yay…