Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to, ya sadar da zumuncinsa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to, ya sadar da zumuncinsa".
Explanation
Benefits
Sakamako yana kasance ne daga jinsin aikin da aka yi, wanda ya sadar da zumuncinsa da kirki da kyautatawa, Allah Zai sadar da shi a rayuwarsa da arzikinsa.
Sadar da zumunci sababi ne na yalwar arziki, kuma sababi ne na tsawon rayuwa, duk da cewa ajali da arziki abin iyakancewa ne, sai dai cewa zai iya zama albarka cikin arziki da rayuwa, sai ya yi aiki a rayuwarsa mafi yawa kuma mafi amfani daga abin da waninsa zai aikata, a wata faɗar aka ce ƙarin arziki da rayuwa ƙari ne na haƙiƙa. Allah ne Mafi sani.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

