”
#58122HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai ci; to, ya ci da damansa, idan zai sha; to, ya sha da damansa, domin cewa Shaiɗan yana ci da hagunsa, kuma yana sha da hagunsa".
”
#58125HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace".
”
#58144HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya ƙetarewa al'ummata abinda ta yi tunanin shi a zuciya, muddin dai bata aikata ba ko ta yi magana ba".
”
#58148HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali".
”
#58188HadeethEnc[Hasan ne]
Daga Bahzu ɗan Hakim daga babansa daga kakansa ya ce: Na ce ya Manzon Allah: Waye wanda zan fi yi wa biyayya? Ya ce: «Mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan babanka, sannan mafi kusa sai mafi kusa».
”
#58218HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuwar Jahiliyya, wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin makauniyar tuta, yana fushi…
”
#58223HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Arfajah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya zo muku alhali al'amarinku gabaɗaya yana hannun mutum ɗaya (kanku a haɗe a ƙarƙashin shugabancin mutum ɗaya), kuma yana son ya tsaga sa…
”
#58227HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Ikramah: Cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ƙona wasu mutane, sai labarin ya kaiwa Ibnu Abbas sai ya ce: Da ace ni ne ba zan ƙonasu ba; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada Ku yi azaba da azabar Allah», da na kashe su…
”
#58240HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah ya yarda da su - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bayan ya jefe al-Aslami sai ya ce: "Ku nisanci wannan ƙazantaccan da Allah Ya yi hani gare su, duk wanda ya zakke musu to ya suturta da suturar Allah kuma…
”
#58259HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda ya sha giya a duniya sai ya mutu alhali shi yana mai dawwama a sh…
”
#64597HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku".
”
#64632HadeethEnc[Ingantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa]
Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi -: Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika shi zuwa Yaman sai ya umarce shi ya karɓi Tabi'i namiji ko mace (wanda yake bin uwarsa kiwo) daga dukkan (shanu) talatin, haka (ya karɓi) Musinnah daga dukkan…