Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sameshi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah
Daga ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, sai ya ce: "Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sameshi a daura da kai,…

