Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiya ne abin gasgatawa: "Lallai cewa halittar dayanku ana tarota a cikin mahaifiyarsa yini arba'in da dare arba'in
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi -: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiya ne abin gasgatawa:
"Lallai cewa halittar dayanku ana tarota a cikin mahaifiyarsa yini arba'in da dare arba'in.
Sannan ya zama gudan jini tamkarsa, sannan ya zama gudan tsoka tamkarsa, sannan a aiko masa da Mala'ika, a yi masa izini da kalmomi hudu, sai ya rubuta arzikinsa da ajalinsa da aikinsa, dan wuta ne ko dan Aljanna ne, sannan ya busa rai a cikinsa.
Lallai dayanku zai yi aiki da aikin 'yan Aljanna har ya zama tsakaninsa da ita bai zamo ba sai zira'i, sai littafi ya rigaya agare shi sai ya yi aiki da aikin 'yan wuta sai yashiga wutar. Kuma cewa dayanku zai yi aiki da aikin 'yan wuta har ya kasance tsakaninsa da ita bai zamo ba sai zira'i, sai littafi ya rigaya akansa, sai ya aikata aikin 'yan aljanna sai ya shigeta".
Explanation
Benefits
Gargadi akan ruduwa da yanayin ayyuka; kadai ayyuka da karshe ne kawai.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

