Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru masu raunin hankula, suna faɗin mafi alherin zancen halitta (suna yawaita karatun Alƙur'ani), zasu fita daga Musulunci kamar yadda kibiya take fita daga abin da aka harba,
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi -: Idan na zantar da ku wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ace in faɗo daga sama shi ya fi soyuwa gareni daga in yi masa (Annabi) ƙarya, idan na zantar da ku a abinda yake tsakanina da ku to l…

