Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru masu raunin hankula, suna faɗin mafi alherin zancen halitta (suna yawaita karatun Alƙur'ani), zasu fita daga Musulunci kamar yadda kibiya take fita daga abin da aka harba,
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi -: Idan na zantar da ku wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ace in faɗo daga sama shi ya fi soyuwa gareni daga in yi masa (Annabi) ƙarya, idan na zantar da ku a abinda yake tsakanina da ku to lallai yaƙi ɗan yaudara ne, na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru masu raunin hankula, suna faɗin mafi alherin zancen halitta (suna yawaita karatun Alƙur'ani), zasu fita daga Musulunci kamar yadda kibiya take fita daga abin da aka harba, imaninsu ba zai ƙetare maƙogwaransu ba, a duk inda kuka gamu da su to ku kashesu, domin kashesu lada ne ga wanda ya kashesu a ranar alƙiyama».
Explanation
Benefits
A cikin hadisin akwai alama daga alamomin Annabta, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin abinda zai faru a bayansa, sai ya faru kamar yadda ya bada labarin shi.
Halaccin yin tauriyya da jirwaye mai kama da wanka a cikin yaƙi, yaudara a cikin yaƙi tana kasancewa ne ta hanyar yin tauriyya, kuma tana kasancewa ta hanyar bazata, da makamancinsu, ba tare da warware alƙawari ba ko (warware) amintarwa ba, saboda zuwan hani akan hakan.
Nawawi ya ce akan (ma'anar) (Suna faɗa daga mafi alherin zancen talikai) Ma'anarsa: A zahirin al'amari kamar faɗinsu: Babu wani hukunci sai na Allah, da makamancinsa daga kiransu zuwa Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
Ibnu Hajar ya ce a cikin faɗinsa (Imaninsu ba ya ƙetare maƙogwaransu): Abin nufi cewa imani bai tabbata a cikin zukatansu ba; domin dukkan abinda ya tsaya a maƙogwaro bai ƙetare shi ba to ba ya kaiwa zuciya.
Alƙali ya ce: Malamai sun yi ijma'i akan cewa Kahawarij da makamantansu cikin 'yan bidi'a da tawaye a duk lokacin da suka yi wa shugaba tawaye suka saɓa ra'ayin jama'a suka raba kawunan mutane to ya wajaba a yaƙesu bayan an yi musu gargaɗi, an gabatar da uzuri garesu.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

