Mafi alherinku zamanina, sannan waɗanda suke biye musu, sannan waɗanda suke biye musu
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Imran ɗan Hussain - Allah - Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mafi alherinku zamanina, sannan waɗanda suke biye musu, sannan waɗanda suke biye musu» Imran ya ce: Ban sani ba shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agatre shi - bayan nan ya ambaci ƙarni biyu ne ko uku, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai a bayanku za'a samu wasu mutane zasu dinga ha'iinci ba'a amince musu ba, sunayin shaida ba tare da an nemi shaidarsu ba, suna bakance ba sa cikawa, kuma ƙiba zata bayyana a cikinsu».
Explanation
Benefits
Ibnu Hajar ya ce: Wannan hadisin ya hukunta cewa sahabbai su zama sun fi tabi'ai, tabai'ai kuma sun fi waɗanda ke binsu, sai dai wannan fifikon shin dangane da tattaron jama'a ne ko ɗaiɗaiku? Wannan abu ne na bincike, amma ra'ayi na biyun (ɗaiɗaiku) shi ne wanda jumhur ɗin malamai suka tafi akai.
Nuni zuwa lazimtar bin hanyar zamaninnika uku na farko; domin cewa wanda zamaninsa ya kusanci zamanin Annabta to shi ya fi falala da ilimi da koyi da shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Bakance: Shi ne mukallafi ya lazimtawa kansa wani aikin ɗa'ar da Mai Shari’a ba ta lazimta masa ba ta hanyar maganar da take nuni a kansa.
Zargin ha'inci da rashin cika alƙawari da rataya da duniya.
Zargin shaida ba tare da an nemi shaidarsu ba idan mai haƙƙin yana sanin hakan, idan ya kasance ba shi da sanin hakan sai ya shiga cikin faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Shin bana baku labari ba da mafi alherin masu shaida shi ne wanda yake zuwa da shaidarsa kafin a tambaye shi ita» Muslim ne ya ruwaito shi .
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

