Ɗan Adam bai cika ƙwarya mafi sharri daga ciki ba, 'yan lomomi su ishi ɗan Adam waɗanda zasu tsaida bayansa, idan ya kasance babu makawa, to ɗaya bisa uku dan abincinsa, da ɗaya bisa uku dan abin shansa, da ɗaya bisa uku dan numfashinsa
Daga Miƙdam ibnu Ma'adikarib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Ɗan Adam bai cika ƙwarya mafi sharri daga ciki ba, 'yan lomomi su ishi ɗan Adam waɗanda zasu tsaida bayansa, idan ya kasance babu…

