Za'a bijiro da fitintinu akan zukata kamar tabarma kara-kara
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance a wurin Umar - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: Waye a cikinku ya ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayanin fitintinu? Sai wasu mutane suka ce: Mu mun ji shi, sai ya ce: Wataƙila ku kuna nufin fitinar mutum a cikin iyalansa da maƙwanbcinsa ? suka ce: Eh, ya ce: Wannan sallah da azimi da sadaka zasu kankaresu, sai dai waye a cikinku ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayani akan wacce take tasowa kamar tasowar kumfar kogi? Huzaifa ya ce: Sai mutane suka yi shiru, sai na ce: Ni, ya ce: ka kyauta kuwa kai ne, Huzaifa ya ce: Na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Za'a bijiro da fitintinu akan zukata kamar tabarma kara-kara, duk zuciyar da aka cakuɗata da su sai ta yi masa baƙin ɗigo, duk zuciyar data musantasu kuwa za’a yi mata farin ɗigo, har su zama akan zukata biyu (nau'i biyu), akan farar zuciya kwatankwacin fal dutse, to wannan fitinar ba zata cutar da ita ba muddin sammai da ƙasa suna nan, ɗayar kuma baƙace ƙirin kamar kifaffiyar ƙwarya, ba ta san wani aikin alheri, kuma bata inkarin wani abin ƙi, sai abinda aka cakuɗa mata na son ranta". Huzaifa ya ce: Kuma na zantar da shi, cewa lallai tsakaninka da su akwai wata kullalliyar ƙofa ta kusa a karya ta, Umar ya ce: Shin karyawa za'a yi kaicanka? Inama dai bude ta za'a yi watakila a dawo da ita, na ce: Kuma na zantar da shi wani labarin da bana galadi ba cewa wannan kofar wani mutum ne da za'a kashe ko ya mutu.
Abu Khalida ya ce: Sai na ce wa Sa'ad: Ya Abu Malik, me ake nufi da Aswad Murbadun? Ya ce: Tsananin fari a cikin baki. Ya ce: Sai na ce: To me ake nufi da al-Kuzul mujakkhiya? ya ce: Wacce aka kife.
Explanation
Akan farar zuciya dan tsananinta akan ƙulla imani, da kuma kuɓutarta daga ɓaci, kuma fitintinu basu danfara da ita ba, kuma ba su yi tasiri a cikinta ba kamar falalin dutse mulmulalle wanda wani abu bai makale a jikin shi ba, dan haka wata fitina ba zata cutar da ita ba , har sai ya gamu da Allah. Ɗaya zuciyar kuma ita ce zuciyar da launinta ya canza zuwa baƙi saboda fitintinu kamar karkatacciya ko juyayyar butar da ruwa ba ya zama a cikinta, to haka wannan zuciyar take wani alheri ko wata hikima ba ta damfare da ita, bata sanin wani abin alheri, kuma bata inkarin wani abin ƙi, sai abinda ta so kuma ranta ya so shi kawai. Huzaifa ya ce wa Umar: Lallai waɗannan fitintinun wani abu ba zai fita daga garesu a cikin rayuwarka ba, kuma tsakaninka da su akwai wata kullalliyar ƙofa ta kusa a karyata, Umar ya ce: Shin karyawa za’a yi karara? inama dai a ce a buɗeta wataƙila ta kasance a dawo da ita sai a kulleta, Huzaifa ya ce: A'a, kai, karyata za’a yi, kuma lallai wannan ƙofar wani mutum ne da za’a kashe ko ya mutu. Kuma abinda na ambace shi labari ne na gaskiya, kuma ba ya cikin littattafan ma'abota littafi biyu (Yahudawa da Nasara), kuma ba ijtihadi ne na wani ma'abocin wani ra'ayi ba, kai daga Hadisin Annabi ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Benefits
Keɓantattun fitintinu idan sun kasance masu danfare da addini ne to ma'abocinsu abin zargi ne; domin su kodai bidi'o'i ne ko kuma saɓo, idan kuma sun kasance masu rataya ne da al'amuran duniya, to su jarrabawa ce ga ma'abocinsu, kuma haƙuri shi ya wajaba a kansa.
Zuciya tana tasirantuwa da fitintinun da suke bijiro mata, wanda ya dace, shi ne wanda Allah Ya shiryar da shi ya tabbata akan shiriya.
Nawawi ya ce: Mai (Littafin) al-Tahrir ya ce: Ma'anar Hadisin: Cewa mutum idan ya bi son ransa ya aikata saɓo sai duhu ya shiga cikin zuciyarsa saboda dukkan saɓon da yake yi, idan ya zama kamar haka sai ya fitunu kuma hasken musulunci ya gushe daga gare shi, zuciya kwatankwacin kofi ne idan aka kifar da shi sai abinda ke cikinsa ya zube, kuma wani abu ba zai shiga cikinsa ba.
Maganar Umar ga Huzaifa: (La aba laka) ma'anarsa: Ka yi ƙoƙari a cikin wannan al'amarin, ka zage dantse ka yi shiri, irin shirin wanda ba shi da wani mataimaki.
Falalar Umar - Allah Ya yarda da shi -, kuma shi ne kullalliyar ƙofar tsakanin mutane da fitina.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

