Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, ko da bawa ne ya shugabance ku, domin cewa wanda ya rayu daga cikinku zai ga saɓani mai yawa, to na horeku da sunnata da kuma sunnar halifofina shiryayyu masu shiryarwa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Najih Irbad ibn Sariyah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mana wa’azi, wa’azin da zukata suka firgita daga gare shi, kuma idanuwa suka zub da hawaye daga gare shi, muka ce: Ya Manzon Allah! kamar wa’azin mai bankwana, ka yi mana wasiyya, sai ya ce: «Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, ko da bawa ne ya shugabance ku, domin cewa wanda ya rayu daga cikinku zai ga saɓani mai yawa, to na horeku da sunnata da kuma sunnar halifofina shiryayyu masu shiryarwa Ku riƙeta da turaman haƙoranku, na haneku daga fararrun al'amura; domin dukkanin bidi'a ɓata ce».
Explanation
Benefits
Kula da wa'azuzzuka da kuma tausasa zukata.
Umarni da bin Halifofi masu shiryarwa su hudu a bayansa, su ne Abubakar da Umar da Usman da Aliyu - Allah Ya yarda da su -.
Hani daga kirikira a Addini, kuma cewa kowacce bidi'a bata ce.
Ji da bi ga wanda ya jibinci al'amarin muminai in ba sabo ba ne.
Muhimmancin tsoron Allah - Mai girma da daukaka - a dukkanin lokuta da halaye.
Sabani mai afkuwane a cikin wannan al'ummar, a yayin faruwarsa to yana wajaba komawa zuwa sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Halifofinsa masu shiryarwa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

