Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai tsanani a bayana, to na horeku da sunnata da sunnar Halifofina shiryayyu
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Irbad dan Sariya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu, sai ya yi mana wa'azi, wa'azi isasshe zukata suka ji tsoro daga gare shi, idanuwa suka zubar da hawaye daga gareshi, aka ce: Ya Manzon Allah ka yi mana wa'azin bankwana to ka yi mana alkawari.
Sai ya ce: 'Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai tsanani a bayana, to na horeku da sunnata da sunnar Halifofina shiryayyu, ku rike su da turamen hakoranku, na haneku da fararrun al'amura, domin cewa kowacce bidi'a bata ce".
Explanation
Benefits
Kula da wa'azuzzuka da kuma tausasa zukata.
Umarni da bin Halifofi masu shiryarwa su hudu a bayansa, su ne Abubakar da Umar da Usman da Aliyu - Allah Ya yarda da su -.
Hani daga kirikira a Addini, kuma cewa kowacce bidi'a bata ce.
Ji da bi ga wanda ya jibinci al'amarin muminai in ba sabo ba ne.
Muhimmancin tsoron Allah - Mai girma da daukaka - a dukkanin lokuta da halaye.
Sabani mai afkuwane a cikin wannan al'ummar, a yayin faruwarsa to yana wajaba komawa zuwa sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Halifofinsa masu shiryarwa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

