Na shiga ni da Mahaifina ga Abu Baraza Al-aslami, sai Mahaifina ya ce da shi:yaya Annabi SAW yake sallar farilla?
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
An rawaito daga Al-minhal Sayar Bn Salama ya ce: (Na shiga ni da Babana ga Abu baraza Al-aslami, sai ya ce da shi yaya Annabi SAW yake Sallar farilla? sai ya ce: ya Kasance yana Sallar Azahar -wacce suke kiranta ta farko- lokacin da Rana ta karya, kuma yana Sallatar La'asar sannan dayan mu ya dawo zuwa Masaukinsa a karshen Madina Rana tana nan, na manta abunda ya ce a Magriba, kuma ya Kasance yana son ya jinkirta Isha wacce muke kiranta Al-atama, kuma ya kasance yana kin ayi bacci kafinta, da kuma yin Magana Bayanta kuma ya kasance yana yana tafiya daga Sallar Asuba lokacin da Mutum zai iya gane na kusa da shi, kuma ya kasance yana Karanta Aya Sttin zuwa Dari.
Explanation
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

