Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na tagulla, suna yakusar fuskokinsu da ƙirazansu da su
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na tagulla, suna yakusar fuskokinsu da ƙirazansu da su, sai na ce: Su waye waɗannan ya Jibril, ya ce: Waɗanan sune waɗanda suke cin naman mutane, kuma suke afkawa cikin mutuncinsu».
Explanation
Benefits
Afkawa cikin mutuncin mutane yana daga yi da mutum da makamancinsa na manyan zunubai.
Al-Ɗaibi ya faɗa a cikin faɗinsa: "Suna yakusa", ya ce: Yayin da yakusar fuska da ƙirji suka zama daga cikin siffofin mata masu kukan mutuwa sai aka sanya hakan sakayyar wanda yake yi da mutane, kuma yake cin mutuncin musulmai, dan sanarwa da cewa su ba sa daga cikin siffofin maza, kai su suna daga cikin siffofin mata a cikin mafi munin hali kuma mafi munin sura.
Wajabcin yin imani da gaibu da kuma dukkanin abinda Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka bada labari da shi.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

