Kaɗai kwatankwacin abokin zama na gari da mummunan abokin zama, kamar maɗaukin almiskine da mai busa zugazugi,
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kaɗai kwatankwacin abokin zama na gari da mummunan abokin zama, kamar maɗaukin almiskine da mai busa zugazugi, maɗaukin alimiski: Kodai ya baka, ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka samu ƙanshi mai daɗi daga gare shi, mai busa zugazugi kuwa: Kodai ya ƙona kayanka, ko kuma ka samu mummunan ƙanshi daga gare shi".
Explanation
Nau'i na farko: Abokin zama da aboki na gari wanda yake shiryarwa ga Allah a abinda a cikinsa akwai yardar Allah, kuma yana taimakawa akan biyayya ga Allah, To kwatankwacinsa kamar mai saida almiski ne, kodai ya baka, ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka samu ka shaƙi ƙanshi mai daɗi daga gare Shi.
Nau'i na biyu: Abokin zama kuma mummunan aboki; wanda yake toshe tafarkin Allah, kuma yana taimako akan aikin saɓo, kuma kana ganin mummunan aiki daga gare shi, kuma yana tsawaita maka zargi dan abokantaka da zama da irinsa, to kwatankwacinsa kamar maƙeri ne wanda yake hura wutarsa; kodai ya ƙona maka tufafi daga tartsatsinsa mai tashi, ko ka samu mummunan wari saboda kusantakarsa.
Benefits
Zaburarwa da kwaɗaitarwa akan zama da ma'abota biyayya da nagarta, da nisantar ma'abota ɓarna da ma'abota munanan ɗabi'u.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

