Akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninka ya kasance yana da ciwo, sai ya kasa haƙuri, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa, jinin bai tsaya ba har sai da ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: BawaNa yayi miNi gaggawa da ransa, (saboda haka) na haramta masa aljanna
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Hassan ya ce: Jundub ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya yi mana hadisi a cikin wannan masallacin, kuma bamu manta ba tun da ya yi mana hadisin, kuma bama jin tsoron cewa Jundub ya yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninka ya kasance yana da ciwo, sai ya kasa haƙuri, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa, jinin bai tsaya ba har sai da ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: BawaNa yayi miNi gaggawa da ransa, (saboda haka) na haramta masa aljanna".
Explanation
Benefits
Bayar da bayanin al'ummun da suka shuɗe da abinda a cikinsa akwai alheri da kuma wa'azi.
Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai tsayuwa a wurin haƙƙoƙin Allah da kuma rahamarSa ga halittarSa inda Ya haramta musu kashe rayukansu, kuma cewa rayuka mallakin Allah ne.
Haramta aikata sabubban da zasu kai zuwa kashe rai, da kuma narko mai tsanani a cikin hakan.
Ibnu Hajar ya ce: Hakan ya yi nuni akan ya yanke hannun ne dan nufin mutuwa ba dan nufin yin maganin da yake kyakkyawan zai yi anfani da shi ba.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

