Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gareta. sai na yi kaffarar rantsuwata, kuma nazowa wanda shi ne mafi alherin
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wasu mutane daga Ash'arawa ina neman ya dauki nauyinmu, sai ya ce:
"Wallahi ba zan dauki nauyinku ba, bani da abinda zan dauki nauyinku" Sannan muka zauna lokacin da Allah Ya so, sai aka zo da wasu rakuma, sai ya yi mana umarni da rakuma uku, lokacin da muka tafi sai sashinmu suka ce da sashi: Allah ba Zai yi mana albarka ba, mun zowa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - muna neman ya dauki nauyinmu sai ya yi rantsuwa cewa ba zai dauki nauyinmu ba sai kuma ya dauki nauyinmu, sai Abu Musa ya ce: sai muka zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai muka ambata masa hakan, sai ya ce: "Ba nine na ɗauki nauyinku ba, a’a Allah ne Ya ɗauki nauyinku, Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gareta. sai na yi kaffarar rantsuwata, kuma nazowa wanda shi ne mafi alherin".
Explanation
Benefits
Halaccin togaciya da fadinsa: In Allah Ya so", bayan rantsuwa, kuma togaciya idan an yi niyya tare da rantsuwa, kuma hakan ya kasance a hade da rantsuwar to kaffara bata wajaba akan wanda ya yi karya rantsuwarsa.
Kwadaitarwa a kan sabawa rantsuwa idan ya ga waninta shi ne mafi alheri daga rantsuwar, kuma ya yi kaffarar rantsuwarsa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

