ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Shi ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci".
Explanation
Benefits
Sababi a hanin (cewa shi ba ya zuwa da alheri); domin ba ya juyar da komai daga hukuncin Allah; kuma kada mai bakancen ya yi zatan cewa samun abinda yake nema ya kasance ne da sababin bakancen, Allah - Maɗaukakin sarki - Mawadaci ne daga hakan.
Kurɗubi ya ce: Wannan hanin bigiransa misali ya ce: Idan Allah Ya warkar da mara lafiya na to na wajabta wa kaina kaza. Ta yadda karhancin yake shi : yayin da ya tsayar da aikin kusanci akan faruwar abinda yake so, ya bayyana cewa shi niyyar neman kusanci ga Allah - Maɗaukakin sarki - ba ta zama tsantsa ba saboda abinda ya bijiro da shi, kai ya shiga hanyar neman canji, kuma ya bayyanar da shi cewa shi da bai warkar da mara lafiyansa ba, da bai yi sadaka da abinda ya rataya akan warkar da shi ba, wannan shi ne halin marowaci, cewa shi ba ya fitar da wani abu daga dukiyarsa sai da wani canji magaggauci da zai yi kari kan abinda ya fitar a galibi.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

