الواقعة
Al-Waqi'ah
The Inevitable
1 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 001
إِذَا وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ
Idan mai aukuwa ta auku.
2 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 002
لَيۡسَ لِوَقۡعَتِهَا كَاذِبَةٌ
Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
3 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 003
خَافِضَةٞ رَّافِعَةٌ
(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
4 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 004
إِذَا رُجَّتِ ٱلۡأَرۡضُ رَجّٗا
Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
5 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 005
وَبُسَّتِ ٱلۡجِبَالُ بَسّٗا
Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
6 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 006
فَكَانَتۡ هَبَآءٗ مُّنۢبَثّٗا
Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
7 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 007
وَكُنتُمۡ أَزۡوَٰجٗا ثَلَٰثَةٗ
Kuma kun kasance nau'i uku.
8 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 008
فَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ
Watau mazõwa dãma*. Mẽne ne mazõwa dãma?
* Mazõwa dãma ko mãsu albarka waɗanda zã a baiwa takardunsu a dãma. Mazõwa hagu ko mãsu shu'umci waɗanda zã a baiwa takardunsu da hagu.
9 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 009
وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ
Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
10 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 010
وَٱلسَّـٰبِقُونَ ٱلسَّـٰبِقُونَ
Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
11 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 011
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلۡمُقَرَّبُونَ
Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
12 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 012
فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
A ckin Aljannar ni'ima.
13 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 013
ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ
Jama'a ne daga mutãnen farko.*
* Jama'a daga mutãnen farko, sũ ne Annabãwan farko da kaɗan daga cikin mutãnen ƙarshe, shi ne Annabi Muhammadu, sallallãhu alaihi wa sallama. Bã a shiga cikin wannan kashi da aiki sai dai da zãɓin Allah. Kuma an rufe ƙõfarsa. Bãbu sauran wani annabi wanda zai zo da wani addini sãbo a bãyan Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.
14 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 014
وَقَلِيلٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ
Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
15 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 015
عَلَىٰ سُرُرٖ مَّوۡضُونَةٖ
(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu.
16 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 016
مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيۡهَا مُتَقَٰبِلِينَ
Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
17 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 017
يَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٞ مُّخَلَّدُونَ
Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
18 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 018
بِأَكۡوَابٖ وَأَبَارِيقَ وَكَأۡسٖ مِّن مَّعِينٖ
Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
19 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 019
لَّا يُصَدَّعُونَ عَنۡهَا وَلَا يُنزِفُونَ
Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
20 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 020
وَفَٰكِهَةٖ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ
Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
21 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 021
وَلَحۡمِ طَيۡرٖ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ
Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.
22 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 022
وَحُورٌ عِينٞ
Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
23 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 023
كَأَمۡثَٰلِ ٱللُّؤۡلُوِٕ ٱلۡمَكۡنُونِ
Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.
24 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 024
جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
25 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 025
لَا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا تَأۡثِيمًا
Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
26 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 026
إِلَّا قِيلٗا سَلَٰمٗا سَلَٰمٗا
Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
27 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 027
وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ
Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
28 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 028
فِي سِدۡرٖ مَّخۡضُودٖ
(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
29 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 029
وَطَلۡحٖ مَّنضُودٖ
Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.
30 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 030
وَظِلّٖ مَّمۡدُودٖ
Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
31 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 031
وَمَآءٖ مَّسۡكُوبٖ
Da wani ruwa mai gudãna.
32 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 032
وَفَٰكِهَةٖ كَثِيرَةٖ
Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.
33 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 033
لَّا مَقۡطُوعَةٖ وَلَا مَمۡنُوعَةٖ
Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
34 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 034
وَفُرُشٖ مَّرۡفُوعَةٍ
Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
35 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 035
إِنَّآ أَنشَأۡنَٰهُنَّ إِنشَآءٗ
Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
36 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 036
فَجَعَلۡنَٰهُنَّ أَبۡكَارًا
Sa'an nan Muka sanya su budurwai.
37 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 037
عُرُبًا أَتۡرَابٗا
Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
38 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 038
لِّأَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
Ga mazõwa dãma.
39 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 039
ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ
Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
40 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 040
وَثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ
Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
41 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 041
وَأَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ
Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
42 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 042
فِي سَمُومٖ وَحَمِيمٖ
Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
43 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 043
وَظِلّٖ مِّن يَحۡمُومٖ
Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
44 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 044
لَّا بَارِدٖ وَلَا كَرِيمٍ
Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.
45 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 045
إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُتۡرَفِينَ
Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
46 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 046
وَكَانُواْ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلۡحِنثِ ٱلۡعَظِيمِ
Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
47 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 047
وَكَانُواْ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ
Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"
48 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 048
أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ
"Shin, kuma da ubanninmu na farko?"
49 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 049
قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَوَّلِينَ وَٱلۡأٓخِرِينَ
Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."
50 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 050
لَمَجۡمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ
"Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."
51 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 051
ثُمَّ إِنَّكُمۡ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلۡمُكَذِّبُونَ
"Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"
52 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 052
لَأٓكِلُونَ مِن شَجَرٖ مِّن زَقُّومٖ
"Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."
53 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 053
فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ
"Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."
54 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 054
فَشَٰرِبُونَ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡحَمِيمِ
"Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."
55 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 055
فَشَٰرِبُونَ شُرۡبَ ٱلۡهِيمِ
"Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."
56 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 056
هَٰذَا نُزُلُهُمۡ يَوۡمَ ٱلدِّينِ
Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
57 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 057
نَحۡنُ خَلَقۡنَٰكُمۡ فَلَوۡلَا تُصَدِّقُونَ
Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
58 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 058
أَفَرَءَيۡتُم مَّا تُمۡنُونَ
Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
59 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 059
ءَأَنتُمۡ تَخۡلُقُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡخَٰلِقُونَ
Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
60 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 060
نَحۡنُ قَدَّرۡنَا بَيۡنَكُمُ ٱلۡمَوۡتَ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ
Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa* ba,
* Ãyã ta 60 haɗe take da ãya ta 61 watau, bã zã Mu kãsa musanya ku da waɗansu mutãne ba su tsaya matsayinku, sa'an nan kũ kuma Mu mayar da ku wata halitta.
61 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 061
عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمۡثَٰلَكُمۡ وَنُنشِئَكُمۡ فِي مَا لَا تَعۡلَمُونَ
A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
62 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 062
وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُولَىٰ فَلَوۡلَا تَذَكَّرُونَ
Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
63 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 063
أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَحۡرُثُونَ
Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
64 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 064
ءَأَنتُمۡ تَزۡرَعُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلزَّـٰرِعُونَ
Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
65 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 065
لَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَٰهُ حُطَٰمٗا فَظَلۡتُمۡ تَفَكَّهُونَ
Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
66 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 066
إِنَّا لَمُغۡرَمُونَ
(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"
67 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 067
بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ
"Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"
68 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 068
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلۡمَآءَ ٱلَّذِي تَشۡرَبُونَ
Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
69 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 069
ءَأَنتُمۡ أَنزَلۡتُمُوهُ مِنَ ٱلۡمُزۡنِ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنزِلُونَ
Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
70 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 070
لَوۡ نَشَآءُ جَعَلۡنَٰهُ أُجَاجٗا فَلَوۡلَا تَشۡكُرُونَ
Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
71 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 071
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي تُورُونَ
Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
72 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 072
ءَأَنتُمۡ أَنشَأۡتُمۡ شَجَرَتَهَآ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنشِـُٔونَ
Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
73 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 073
نَحۡنُ جَعَلۡنَٰهَا تَذۡكِرَةٗ وَمَتَٰعٗا لِّلۡمُقۡوِينَ
Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
74 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 074
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ
Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
75 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 075
۞فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ
To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
76 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 076
وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٞ لَّوۡ تَعۡلَمُونَ عَظِيمٌ
Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
77 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 077
إِنَّهُۥ لَقُرۡءَانٞ كَرِيمٞ
Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
78 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 078
فِي كِتَٰبٖ مَّكۡنُونٖ
A cikin wani littafi tsararre.
79 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 079
لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُطَهَّرُونَ
Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
80 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 080
تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
81 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 081
أَفَبِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَنتُم مُّدۡهِنُونَ
Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
82 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 082
وَتَجۡعَلُونَ رِزۡقَكُمۡ أَنَّكُمۡ تُكَذِّبُونَ
Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
83 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 083
فَلَوۡلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلۡحُلۡقُومَ
To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
84 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 084
وَأَنتُمۡ حِينَئِذٖ تَنظُرُونَ
Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
85 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 085
وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُبۡصِرُونَ
Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
86 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 086
فَلَوۡلَآ إِن كُنتُمۡ غَيۡرَ مَدِينِينَ
To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
87 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 087
تَرۡجِعُونَهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.*
* Idan kun kasance mãsu gaskiya ga da'awar rashin Tãshin Ƙiyãma, to, ku yi ƙõƙarin hana mutuwa ga mutãne dõmin ku hana cikar alkawarin tayarwa a bãyan mutuwa.
88 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 088
فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ
To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
89 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 089
فَرَوۡحٞ وَرَيۡحَانٞ وَجَنَّتُ نَعِيمٖ
Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
90 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 090
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
91 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 091
فَسَلَٰمٞ لَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
92 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 092
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ
Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
93 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 093
فَنُزُلٞ مِّنۡ حَمِيمٖ
Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
94 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 094
وَتَصۡلِيَةُ جَحِيمٍ
Da ƙõnuwa da Jahĩm,
95 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 095
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلۡيَقِينِ
Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
96 - Al-Waqi'ah (The Inevitable) - 096