العاديات

 

Al-'Adiyat

 

The Courser

1 - Al-'Adiyat (The Courser) - 001

وَٱلۡعَٰدِيَٰتِ ضَبۡحٗا
Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.

2 - Al-'Adiyat (The Courser) - 002

فَٱلۡمُورِيَٰتِ قَدۡحٗا
Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.

3 - Al-'Adiyat (The Courser) - 003

فَٱلۡمُغِيرَٰتِ صُبۡحٗا
Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.

4 - Al-'Adiyat (The Courser) - 004

فَأَثَرۡنَ بِهِۦ نَقۡعٗا
Sai su motsar da ƙũra game da shi.

5 - Al-'Adiyat (The Courser) - 005

فَوَسَطۡنَ بِهِۦ جَمۡعًا
Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.

6 - Al-'Adiyat (The Courser) - 006

إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٞ
Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

7 - Al-'Adiyat (The Courser) - 007

وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٞ
Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka.

8 - Al-'Adiyat (The Courser) - 008

وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلۡخَيۡرِ لَشَدِيدٌ
Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.

9 - Al-'Adiyat (The Courser) - 009

۞أَفَلَا يَعۡلَمُ إِذَا بُعۡثِرَ مَا فِي ٱلۡقُبُورِ
Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.

10 - Al-'Adiyat (The Courser) - 010

وَحُصِّلَ مَا فِي ٱلصُّدُورِ
Aka bayyana abin da ke cikin zukata.

11 - Al-'Adiyat (The Courser) - 011

إِنَّ رَبَّهُم بِهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّخَبِيرُۢ
Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?

Scroll to Top