”
#5796HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Nana Aisha Allah Ya yarda da ita, matar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta ta ce: Lalle sassauci ba ya kasance wa a komai sai ya ƙara masa kyau, kuma ba a cire shi a komai sai ya aibanta shi.
”
#5797HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ya ke Aisha lallai Allah Mai tausasawa ne kuma Yana son tausasawa, Yana bayarw…
”
#5799HadeethEnc[Ingantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa]
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin mai azumi da mai tsayuwar dare.
”
#5800HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ga mai tabo mai tabon Abdulƙais: «Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana».
”
#5802HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai wanda ya fiku soyuwa a gare ni kuma mafi kusancinku mazauni a ranar AlKiyama (su ne) mafi kyawunku halayya, kuma mafi ƙinku a gare ni, kuma mafi nisanta…
”
#5803HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi Bn Amr -Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taɓa kasance wa mai alfasha ba, ko mai ƙoƙarin alfasha ba, ya kasance yana cewa: Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku.
”
#5804HadeethEnc[Hasan ne]
An rawaito daga Abu Umama Al-bahili -Allah ya yarda da shi- daga Annabi: "Nine shugaban wani gida a cikin Dausayin Al-jannah ga wanda ya bar jayayya ko da kuwa shi ne Maigaskiya,, Kuma da wani gida cikin tsakiyar Al-janna ga wanda ya bar Karya kuma koda kuwa yana mai Ra…
”
#5812HadeethEnc[Sanadi nsa Hasan ne]
An karbo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- An tambayi Annabi game da abu mafi yawa da yake shigar da Mutane" Al-janna? ya ce: Tsoron Allah da kyawawan Halaye, kuma aka tambaye shi game da abu mafi yawa da yake jefa Mutane wuta sai ya ce Baki da Farjin su"
”
#5866HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora.
”
#6005HadeethEnc[Ingantacce ne]
An rawaito daga Jabir Allah ya hyarda da shi daga Annabi cewa shi idan yayi niyyar yaki sai ya ce: "Ya ku Jama'ar Muhajirai da Mutanen Madina, Lallai cewa daga cikin ku akwai wasu Mutane basu da Dukiya, ko Dangi, saboda haka wani daga cikinku ya hadu da Biyu ko Uku"
”
#6103HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace».
”
#6141HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi Amincin Allah a gare shi ya ce: "Bawa ba zai taba kaiwa Matakin Masu tsoron Allaba har sai ya bar abunda babu laifi a cikinsa"