Za’a zo da mutum ranar Alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin cikinsa su fita, sai ya kewaya da su kamar yadda jaki yake kewaye da dutsen nika
Daga Usama ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An ce masa: Shin ba zaka shiga gurin Usman ba ka yi masa magana? sai ya ce: Shin kuna ganin cewa ni ba za yi masa magana ba har sai na fada muku? wallahi hakika na yi masa magana tsakanina da shi, ba tare da na buɗe k…

