Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai.
Search and read verified Prophetic hadeeth translations, explanations, benefits, categories and source attribution. Page 134.
Smart instant results tolerate minor spelling mistakes, with every filter in one place.
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai.
Daga Abdullahi ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya ji wani abu a cikinsa, sai ya rikitar da shi cewa shin wani abu ya fita daga gare shi ko a'a, to, kada ya fita daga masallaci har sai…
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa".
Daga Ƙais ɗan Asim - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulunci, sai ya umarceni da in yi wanka da ruwa da magarya.
Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Ina shaid…
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi ma…
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan: {Ku tsai da sallah domin tunani} [Daha: 14".
Daga Mahmud ɗan Labid - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Usman ɗan Affan ya yi nufin gina masallaci sai mutane suka ƙi hakan, suka so ya bar shi a kan yadda yake, sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya gina masal…
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma".
Daga Abu Katada AsSulami - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna".
Daga Abu Humaid ko daga Abu Usaid ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa".
Follow any language without creating an account.