Lallai waɗannan masallatan badan fitsari aka yi su ba, ko dan ƙazanta , kawai su dan ambatan Allah ne - Mai girma da ɗaukaka, da sallah da kuma karatun alƙur'ani
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana muna cikin masallaci tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ga wani balaraben ƙauye ya zo, sai ya miƙe yana fitsari a cikin masallaci, sai sahabban Manzon Allah - tsira da…

