"Lallai Kabilar Ash'ariyawa idan Mujinsu ya Mutu a wajen yaki, ko Abincin Iyalansu ya ragu a Madina"
An rawaito daga Abu Musa Al-Ash'ari -Allah ya yarda da shi- ya ce Annabi SAW ya ce: "Lallai Kabilar Ash'ariyawa idan Mujinsu ya Mutu a wajen yaki, ko Abincin Iyalansu ya ragu a Madina sai su hada abunda yake wurin su a cikin Zani daya, sannan sai su raba shi tsakaninsu…

