Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha, to ya cike aziminsa, kaɗai Allah ne Ya ciyar da shi kuma Ya shayar da shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha, to ya cike aziminsa, kaɗai Allah ne Ya ciyar da shi kuma Ya shayar da shi".

