Mata sun kasance idan Mijinta ya Mutu: sai ta shiga Dan akurkin Da ki, kuma tasanya Mafi mufi daga cikin kayanta kuma babu ruwanta da Turare ko wani abun Ado har sai ta cika shekar, sannan sai azo da wata Dabba-Jaki ne ko Tsuntsu ko Akuya- sai fansheta da shi.
Daga Ummu Salama-Allah ya yarda da ita- daga Annabi: "Wata Mata tazo wajen Manzon Allah sai ta ce: Ya Manzon ALlah, Lallai cewa 'Diyata Mijinta ya mutu ya barta, kuma ga shi tana fama da ciwon Ido shin ta iya sanya Kwalli? sai ya ce: AA Sau biyu ko Sau Uku sannan ya ce:…

