Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna" sai wani mutum ya ce: Koda wani abune ɗan kaɗan ya Manzon Allah? ya ce: "Koda kara ne na itaciyar ƙirya
Daga Abu Umama Iyas ɗan Sa'alaba alHarisi - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna"…

