Shin bakwa amince mini ba alhali ni ne amintaccen wanda ke sama, labarin sama yana zo mini safiya da yamma
Daga Abu Sa'idul Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya aikewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani gutsire na zinare a cikin wata fatar da aka jeme da ƙwallan bagaruwa, ba'a gama tace shi…

