Ya kai yaro! zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka same shi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abul Abbas, Abdullahi ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wata rana, sai ya ce: «Ya kai yaro! zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka same shi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa da ace al'umma za su taru a kan su amfaneka da wani abu, ba za su amfaneka ba sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta maka, da za su taru kuma a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su cutar da kai ba, sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta a kanka; an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe». A cikin wata riwayar da ba ta Tirmizi ba: «Ka kiyaye Allah zaka same shi a gabanka, ka nemi sanin Allah a lokacin wadata zai taimakeka a cikin tsanani, ka sani cewa abin da ya kuskure maka bai zama zai sameka ba, abin da kuma ya sameka bai zama zai kuskure maka ba, ka sani cewa nasara tana tare da haƙuri, kuma yaye baƙin ciki yana tare da farin ciki, kuma sauƙi yana tare da tsanani».
Explanation
Benefits
Sakamako yana kasancewa daga irin aikin da aka yi.
Umarni a kan dogaro ga Allah, da tawakkali gare shi ba da waninsa ba, madalla da Shi a matsayin wakili.
Imani da hukunci da ƙaddara da yarda da shi, kuma Allah Ya ƙaddara kowane abu.
Wanda ya tozarta umarnin Allah, to, Allah Zai tozarta shi ba kuma zai kiyaye shi ba.
Bushara mai girma cewa mutum idan tsanani ya same shi to ya saurari sauƙi.
lallashin bawa a lokacin faruwar musiba, da rasa abin da ake so a cikin faɗinsa: «Ka sani cewa abin da ya sameka bai zama zai kuskureka ba, abin da kuma ya kuskureka to bai zama zai sameka ba» to jumal ta farko bada haƙuri ce a lokacin faruwar wani abin ƙi, ta biyu kuma bada haƙuri a kokacin rasa abin da ake so.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

