Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Cewa shi ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah; Shin bana nuna maka wata mace daga cikin 'yan aljanna ba? na ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar da ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Ni ina farfaɗiya kuma inayin tsirara, to ka roƙamin Allah, ya ce: «Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki» ta ce: Zan yi haƙuri, ta ce : To cewa inayin tsirara to ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara, sai ya roƙa mata.
Explanation
Benefits
Nawawi ya ce: A cikin sa akwai dalili akan cewa farfaɗiya ana bada lada a kanta mafi cikar lada.
Kamewa da kunyar matan sahabbai, da kuma kwaɗayinsu akan suturta - Allah Ya yarda da su -, wannan matar ta kasance mafi yawan abinda take jin tsoro shi ne wani abu ya yaye daga jikinta.
Ibnu Hajar ya ce: Lallai yin riƙo da tsanani shi yafi daga yin riƙo da rangwami ga wanda ya san cewa akan kansa zai iya, kuma ba zai yi rauni ba saboda lazimtar tsanani.
Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa cewa maganin cututtuka gaba ɗayansu shi ne addu'a da kuma komawa zuwa ga Allah ya fi tasiri kuma ya fi amfani daga magani da ƙwayoyi, kuma cewa tasirin hakan da kuma tasirin jiki daga gare shi ya fi girma daga tasirin magungunan jiki, sai dai kaɗai yana tasiri ne da al'amura biyu: Na farkonsu ta ɓangaren wanda illar ta sama shi ne gaskiyar nufi, ɗayan kuma ta ɓangaren mai yin maganin, shi ne ƙarfin niyya da kuma ƙarfin zuciyarsa da tsoron Allah da kuma dogara, Allah ne Mafi sani.
Ibnu Hajar ya ce; A cikinsa akwai dalili akan halaccin barin yin magani.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

