Kada ku tsine masa, na rantse da Allah ban san wani abu daga gare shi ba sai dai yana son Allah da ManzonSa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sunansa Abdullahi, kuma ya kasance ana yi masa laƙabi da jaki, ya kasance yana sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dariya, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ya yi masa bulala saboda giya, sai aka zo da shi wata rana sai ya sa aka yi masa bulala, sai wani mutum daga cikin mutanen ya ce: Ya Allah Ka tsine masa, ina mamakin yawan abin da ake zuwa da shi saboda shi?! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku tsine masa, na rantse da Allah ban san wani abu daga gare shi ba sai dai yana son Allah da ManzonSa".
Explanation
Benefits
Mai aikata babban laifi idan ya mutu alhali shi yana nacewa akan wani abu na laifin, to yana ƙarƙashin mashi'a, idan Allah Ya so Ya yi masa gafara idan Ya so kuma Ya yi masa azaba, babu wani mutum daga cikin musulmai da za'a dawwamar da shi a cikin wuta.
Hanin tsinewa mashayin giya da sunansa; dan yi wuwar samuwar wani abu mai hanawa daga riskuwar tsinuwar; domin tsinewa wani mutum da sunansa da yi masa mummunar addu'a zai iya sa shi ci gaba, ko ya sa shi yanke ƙauna daga karɓar tuba.
Halaccin tsinewa wanda ba’a ayyana sunansa ba wanda kuma ya siffantu da hakan.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

