Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".
Explanation
Benefits
Yaudarar da aka yi narko a kanta ta ƙunshi dukkan wanda ya amince maka akan jini, ko mutunci, ko sirri, ko dukiya sai ka ha'ince shi, ka kuma saɓawa zatinsa a cikin amanarka.
AlƘurɗubi ya ce: wannan magana ce daga gare shi zuwa ga larabawa da irin abinda suke aikatawa; domin su sun kasance suna ɗaga farar tuta dan cika alƙawari, suna ɗaga baƙar tuta kuma dan yaudara, dan su zargi mayaudari, sai Hadisin ya hukunta afkuwar irin haka ga mayaudari; dan ya shahara da siffarsa a taron alƙiyama, kuma al’umma da suke a filin alƙiyama su zarge shi.
Ibnu Hajar ya ce: Kuma a cikinsa mutane za'a kirasu ranar alƙiyama (tare da sunayen) iyayen su; saboda faɗinsa: "Wannan ce yaudarar wane ɗan wane".
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

