Wasu mutane daga Ukl ko Urainah suka zo (wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -), sai suka ƙyamaci zama a Madina
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wasu mutane daga Ukl ko Urainah suka zo (wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -), sai suka ƙyamaci zama a Madina sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce su suje gurin raƙuman (zakka), kuma su sha fitsarinsu da nononsu, sai suka tafi, lokacin da suka samu lafiya sai suka kashe mai kiwon (dabbobin) Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suka kora dabbobin, sai labari ya zo a farkon yini, sai ya aika aka bi bayansu, lokacin da rana ta ɗaga sai aka zo da su, sai ya yi umarni a yanke hannayensu da ƙafafuwansu, kuma aka tsire idanuwansu, aka jefasu a cikin zafin rana, suna neman a shayar da su ruwa amma ba'a shayar da su ba. Abu Ƙilabah ya ce: Waɗannan sun yi sata sun yi kisa, sun kafirta bayan sun yi imani, sun yaƙi Allah da ManzonSa.
Explanation
Benefits
Halaccin magani da nonon rakuma da kuma fitsarinsu.
Shar'ancin yin tamka (a yi wa mutum yadda ya yi wa wani) a cikin ƙisasi, kuma hani akan musla (daddatsa mutum) abin ɗauka ne ta hanyar da bata sakayya ko ƙisasi ba.
Kashe jama'a idan sun kashe mutum ɗaya daidai ne sun kashe shi ta hanyar kisan gilla ne ko kuma ta hanyar fashi.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

