Da a ce sun shigeta da ba zasu fita daga cikinta ba har zuwa ranar alƙiyama; biyayya tana kasancewa ne kawai a aikin alheri
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki wata ƙaramar runduna sai ya shugabantar da wani mutum daga cikin mutanen Madina, kuma ya umarcesu da su yi masa biyayya, sai (mutumin) ya yi fushi, sai ya ce: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai umarce ku ku bini ba? suka ce: Ya umarcemu. (Sai) Ya ce: Ku haɗa mini itatuwa, sai suka haɗa masa, sai ya ce: Ku kunna wuta, sai suka kunnata, sai ya ce: Ku shigeta, sai suka yi niyyar (shiga), sai wasu daga cikinsu suka riƙe wasu, suna cewa: Mun gujewa wuta ne zuwa wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, basu gushe ba har sai da wutar ta mutu, sai fushinsa ya gushe, sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: «Da a ce sun shigeta da ba zasu fita daga cikinta ba har zuwa ranar alƙiyama; biyayya tana kasancewa ne kawai a aikin alheri».
Explanation
Benefits
Mai saɓo mai tauhidi an yi masa alkawarin narko da wuta, amma Allah zai iya gafarta masa.
Halaccin sanya shugaba a cikin yaƙi, haka nan a halin tafiya.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

