Ku barta lallai ita (ɗabi'a ce) mai wari
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Jabir Ibnu Abdullah -Allah Ya yarda da su - ya ce: Mun kasance a cikin wani yaƙi, sai wani mutum daga cikin Muhajirun ya daki bayan wani mutum daga cikin mutanen Madina, sai mutumin Madina ya ce: Yaku mutanen Madina ku kawo mini agaji, wanda ya yi hijira kuma ya ce: Yaku muhajirai ku kawo mini agaji, sai Allah Ya jiyar da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Mene ne wannan?» sai suka ce: Wani mutum ne daga Muhajirun ya daki bayan wani mutum daga cikin mutanen Madina, sai mutumin Madinan ya ce: Yaku mutanen Madina ku kawo mini agaji, wanda ya yi hijira kuma ya ce: Yaku Muhajirun kukawo mini agaji, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ku barta lallai ita (ɗabi'a ce) mai wari ». Jabir ya ce: Mutanen Madina sun kasance a lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina sun fi yawa, sannan Muhajirun suka yi yawa bayan nan, sai Abdullahi Ibnu Ubay ya ce: Shin sun aikata kuwa, wallahi idan muka koma Madina sai maɗaukaka sun fitar da maƙasƙanta, sai Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah ka barni in daki wuyan wannan munafikin, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «ka bar shi, kada mutane suce lallai (Annabi) yana kashe sahabbansa».
Explanation
Benefits
Gargaɗarwa daga yin ƙungiyancin ƙarya da kuma tsoratarwa daga abin ƙyama mara kyau.
Hani daga dukkanin abin da yake haifar da gaba da kuma ƙiyayya.
Nawawi ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci hakan da da'awa irin ta Jahiliyya ne dan yaƙi hakan ne, domin hakan ya kasance akan abin da Jahiliyya suke a kansa ne na neman ɗauki da ƙabilu a cikin al'amuran duniya da abubuwan da ke rataye da su, a Jahiliyya sun kasance suna ɗaukar fansarsu da ta'assubanci da kuma ƙabilu, sai Musulunci ya zo ya ɓata hakan, ya rarrabe bayanai da hukunce-hukunce na shari'a, idan wani mutum ya yi ta'addanci akan wani sai alƙali ya yi hukunci a tsakkaninsu, ya kuma lazimta masa abin da zalincinsa ya hukunta kamar yadda ya tabbata daga ƙa'idojin Musulunci.
Sindi ya ce: Sai ya bayyana cewa nasara dan kasancewar sa ne daga ƙabilarsa kamar yadda ma'abota Jahiliyya suke akai to ɓatacce ne. Dan haka babu wata fuska akan kowane mutum ya kira ƙabilarsa, amma taimakon gaskiya to abin nema ne kuma lazimi ne akan kowane mumini daidai ne ya kasance daga ƙabilarsa ne ko kuma a'a.
Abin da munafukai suke a kansa na magana mara kyau da kuma yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - ƙarfin hali.
Abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa na tsananin juriya da kuma haƙuri akan abin da yake samunsa na cutarwar munafukai.
Gargaɗarwa akan dukkanin aikin da a cikinsa akwai kore mutane daga shiga cikin Addinin Musulunci, saboda haka ne Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana a kashe munafukai dan kada mutane su dinga cewa: Lallai (Annabi) Muhammad yana kashe sahabbansa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

