Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi sallar Asuba sai ya zauna a wurin sallarsa har sai rana ta ɓullo tana ɗage
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Jabir Ibnu Samura - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi sallar Asuba sai ya zauna a wurin sallarsa har sai rana ta ɓullo tana ɗage, kuma ya ce: Ya kasance ba ya tashi daga wurin da ya yi sallar Asuba har sai rana ta ɓullo, idan rana ta ɓullo sai ya tashi, kuma sun kasance suna tattaunawa sai su shiga labari cikin al'amarin Jahiliyya, sai su yi dariya shi kuma ya yi murmushi.
Explanation
Benefits
Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa na kyawawan dabi’u da tattausan lamari, inda ya kasance yana zama tare da sahabbansa, yana sauraran zancensu da hikayoyinsu kuma yana yin murmushi tare da su.
Halaccin yin hira da ambatan kwanukan Jahiliyya a cikin masallaci.
Halaccin dariya da murmushi; domin cewa abin da aka hana shine yawan dariya.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

