Na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi fitsari, sannan ya yi alwala kuma ya yi shafa akan huffinsa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ibrahim al-Nakha'i daga Hammam Ibnul Haris ya ce: Jarir ya yi fitsari, sannan ya yi alwala ya yi shafa akan huffinsa, sai aka ce: Ya kake yin haka? ya ce: Eh, Na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi fitsari, sannan ya yi alwala kuma ya yi shafa akan huffinsa. Al-A'amash ya ce: Ibrahim ya ce: Wannan hadisin yana ƙayatar da su; domin musuluntar Jarir, ta kasance ne bayan saukar (Suratul) Ma'idah.
Explanation
Benefits
Nawawi ya ce: Dukkanin waɗanda ake la'akari da su a cikin Ijma'i sun yi Ijma'i akan halaccin shafa akan huffi a halin tafiya da zaman gida, daidai ne hakan ya kasance dan wata buƙata ne ko dan waninta, haka ma ya halatta ga macen da ta lazimci gidanta da kuma mai cutar shama jika wanda ba ya iya tafiya.
Falalar Jarir Ibu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - yadda ya zama mai yalwar ƙirji, yana jure inkarin ɗalibansa a kansa, koda sun kasance masu kuskure ne.
Raddi akan wanda ya yi inkarin shafa akan huffi kuma ya yi da'awar cewa shi an shafe hukuncin; domin cewa hadisin Jarir - Allah Ya yarda shi - ya yi jinkiri akan ayar alwala.
Bayanin cewa yana kamata ga wanda wani ya yi masa inkari, kuma ya kasance yana ƙudirce ingancinsa cewa kada ya yi fushi akan wanda ya yi masa inkari, kuma ya tattauna da shi gwargwadan zatansa, kai ya bayyanar masa madogararsa a kan hakan da abin da yake mafi kyau.
Kafa hujja da tarihi a lokacin buƙatuwa zuwa gare shi .
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

