Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa jujin wasu mutane, sai ya yi fitsari a tsaye,
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa jujin wasu mutane, sai ya yi fitsari a tsaye, sai na yi nesa, sai ya ce: "ka kusanto" sai na kusanto har na tsaya daura da maƙyangymansa sai ya yi alwala sai ya yi shafa akan kuffinsa biyu.
Explanation
Sai Huzaifa ya yi nesa da shi, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa: Ka kusanto, sai Huzaifa ya kusanto gare shi har ya tsaya a bayansa daura da ƙarshen diga-digansa; dan ya zama kamar kariya gare shi daga kallonsa a wannan halin.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi alwala, lokacin wanke ƙafafuwansa biyu, sai ya wadatu da shafa akan kuffinsa biyu - su ne abinda ake ɗaurawa a ƙafa na fata mara kauri da makamancinta kuma yana zama mai suturce idan sawu - kuma bai ciresu ba.
Benefits
Halaccin yin fitsari a tsaye da sharaɗin kada wani fitsarin ya same shi.
Yadda annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agre shi - ya nemi juji, shi ne bola da shara domin cewa su a galibi masu sauƙi ne fitsari ba zai dawowa mai yin fitsarin ba.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

