Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ruwaito shi Marfu'i: A cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi} [al-haj: 25] ya ce: "Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi".
Explanation
[al-Hajj: 25], ya ce: Da ace wani daga cikin mutane zuciyarsa zata zantar masa cewa ya yi nufin aikata wani mummunan aiki a cikin Haramin Makka wanda zai halatta abinda Allah Ya haramta masa a cikinsa na haram da harshe ne ko kisa da gangan to cewa hakan zalinci ne, kuma da a ce ƙudirin niyyar a birnin Adan ne a cikin (kasar) Yaman to lallai shi mai cancantar Allah Ya azabtar da shi ne da azaba mai raɗaɗi saboda hakan, koda kuwa bai aikata shi ba, niyyar hakan kawai ta ishe shi .
Benefits
Al-Sa'adi ya ce: A cikin wannan ayar mai girma, akwai wajabcin ganin alfarmar Harami, da tsananin girmama shi, da gargaɗarwa daga nufin yin saɓo a cikinsa da kuma aikata (saɓon).
Al-Dahhak ya ce: Lallai mutum zai yi niyyar aikata kuskure a Makka alhali shi yana wata ƙasar daban sai arubuta masa (laifin) alhali bai aikata laifin ba.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

