Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune kafirai}
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da:
{Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune kafirai} [al-Ma'idah: 44], da {Waɗannan sune azzalimai} [al-Ma'ida: 45] da kuma {Waɗannan sune fasiƙai} [al-Ma'ida: 47].
ya ce: Ibnu Abbas ya ce: Allah Ya saukar da ita ne saboda ƙungiyoyi biyu daga cikin Yahudawa, ɗayarsu ta kasance ta rinjayi ɗayar a lokacin Jahiliyya, har suka yadda suka yi sulhu akan cewa dukkanin wadda aka kashe to wacce ta yi rinjayen (babbar kabilar) ta kashe shi daga cikin ƙasƙantacciya (wacce aka yi nasara a kanta) to diyyarsa ita ce Wusƙi hamsin, kuma dukkanin wadda aka kashe wadda ƙasƙantacciyar ta kashe shi daga mai rinjayen to diyyarsa ita ce Wusƙi ɗari, sun kasance akan haka har Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina, dukkanin ƙungiyoyi biyun suka miƙa wuya ga zuwan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wannan lokacin bai yi rinjaye galaba, kuma bai haɗasu a kansa ba, shi yana cikin sulhu, sai ƙasƙantacciyar ta kashe wani daga cikin mai rinjayan, sai mai rinjayen ta aika zuwa gurin ƙasƙantacciyar: Ku aiko mana da Wusƙi ɗari, sai ƙasƙantacciyar ta ce: Shin wannan ya kasance ne a cikin ƙabilu biyu kawai Addininsu ɗaya, nasabarsu ɗaya, garinsu ɗaya, diyyar sashinsu rabin diyyar sashi ce? Mu ɗin nan mun baku wannan ne kawai dan zalincinku a garemu, da rinjayen da kuka yi mana, amma tunda (Annabi) Muhammad ya zo to baza mu baku hakan ba, sai yaƙi ya kusa ya kunnu a tsakaninsu, sannan suka yarda su sanya Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tsakaninsu, sannan wacce ta yi galabar ta ambata sai ta ce: Wallahi (Annabi) Muhammad ba zai baku daga cikinku ninkin abin da suke basu daga garesu ba, kuma haƙiƙa sun yi gaskiya, ba su bamu wannan ba sai dan zalincin da muke yi, da kuma rinjayarsu da muka yi, dan haka ku yi dassi zuwa ga (Annabi) Muhammad wanda zai binciko muku ra'ayinsa: Idan ya baku abin da kuke so to sai ku sanya shi mai hukunci, idan kuma bai baku ba sai ku kiyaye shi, ba zaku sanya shi mai hukunci ba, sai suka yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dassin wasu mutane daga cikin munafukai dan su basu labarin ra'ayin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai Allah Yaba ManzonSa labarin gabaɗayan al'amarinsu da kuma abin da suka yi nufi, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Yakai Manzo kada waɗanda suka yi gaggawa cikin kafirci daga waɗanda suka ce mun yi imani su baƙanta maka rai}[al-Ma'ida: 41] har zuwa faɗinSa: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune fasiƙai}[al-Ma'idah: 47] sannan ya ce: Wallahi ta sauka ne a cikin sha'aninsu, kuma sune Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yake nufi.
Explanation
Benefits
Makircin Yahudawa da kuma zalincinsu har akan kansu.
Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya bada labarin cewa Yahudawa wulaƙanci ya tabbata garesu a duniya da kuma azaba mai raɗaɗi a lahira.
Rashin yin hukunci da abin da Allah Ya saukar da kuma kin yarda da hukuncin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dalili ne akan kafirci da zalinci da kuma fasiƙanci.
Haɗarin munafukai da kuma taimakekeniyarsu tare da Yahudawa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

