Yana daga kyan Musuluncin mutum yabar abin da babu ruwansa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Yana daga kyan Musuluncin mutum yabar abin da babu ruwansa».
Explanation
Benefits
Barin maganagnu marasa anfani da ayyuka dalili ne akan cikar Musuluncin mutum.
Kwaɗaitarwa akan shagltuwa a kan abin da ya shafi mutum na sha'anin Addininsa da duniyarsa, idan yana daga kyan Musuluncin mutum ya bar abin da bai shafe shi ba, to yana daga kyawunsa ya shagaltu a cikin da ya shafe shi .
Ibnul Ƙayyim - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tattaro tsantseni gabaɗayansa a cikin kalma ɗaya, sai ya ce: «Yana daga kyan Musuluncin mutum ya bar abinda babu ruwansa» to wannan ya game barin abin da bai shafe shi ba: Na magana, da kallo, da sauraro, da kamu, da tafiya, da tinani, da sauran motsi na zahiri da na baɗini, wannan ita ce kalma mai warkarwa a cikin tsantseni.
Ibnu Rajab ya ce; Wannan hadisin asali ne na tushen ladabi.
Kwaɗaitarwa akan neman ilimi; domin da shi ne mutum yake sanin abin da ya shafe shi da kuma abin da bai shafeshi ba.
Umarni da aikin alheri da hani na abin ƙi, da kuma nasiha daga abin da ya shafi mutum; domin cewa shi abin umarta ne da su.
Yana shiga cikin gamewar ma'anar hadisin: Nisanta daga abin da bai shafi mutum ba na abin da Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta da kuma abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ƙi shi, haka nan abin da ba'a buƙatuwa zuwa gareshi na al'amuran lahira, kamar haƙiƙanin gaibu da rarrabe-rarraben hukunci a cikin halitta da umarni, daga cikinsu akwai tambaya da bincike game da mas'alolin da aka ƙaddara da waɗanda ake sa ran zasu faru waɗanda ba su faru ba, koma basu kusa su faru ba, koma ba'a suranta faruwarsu ba.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

