Ka tafi zuwa gareshi ka ce masa: Lallai kai ba ka cikin 'yan wuta, sai dai kana daga cikin 'yan aljanna
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi Lallai Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nemiSabitu ɗan Ƙais (domin bai ganshi ba) sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan samo maka labarinsa, sai ya zo masa sai ya same shi a zaune a gidansa ya sunkuyar da kansa, sai ya ce: Meke damunka? sai ya ce: Sharri, ya kasance yana ɗaga sautinsa sama da sautin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, to, haƙiƙa aikinsa ya ɓaci, kuma shi yana daga 'yan wuta.
Sai mutumin ya zo sai ya ba shi labarin cewa kaza da kaza, sai ya dawo a karo na ƙarshe da babban albishir, sai ya ce: "Ka tafi zuwa gareshi ka ce masa: Lallai kai ba ka cikin 'yan wuta, sai dai kana daga cikin 'yan aljanna".
Explanation
Sai mutumin ya dawo zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanar da shi da hakan, sai Annabi - tsaira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce shi ya koma wa Sabitu ɗan Ƙais ya yi masa albishir da cewa shi ba ya daga 'yan wuta, sai dai yana daga 'yan aljanna, domin cewa ya kasance mai babbar murya ne a halitta, domin shi ya kasance mai huɗubar Manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. kuma mai yi wa mutanen Madina huɗuba.
Benefits
Damuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbai da bibiyarsa garesu.
Tsoron sahabbai - Allah Ya yarda da su - game da ɓacin aikinsu.
Wajabcin ladabi wajen yi masa magana - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a rayuwarsa, da ƙanƙan da muryoyi a lokacin jin sunnarsa bayan ya rasu.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

