Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai cewa ni ina sallah kuma ina bacci, ina azimi ina buɗe baki, kuma ina auren mata, wanda ya ƙi sunnata to ba ya tare da ni
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun tambayi matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikinsa a ɓoye? sai sashinsu ya ce: Ba zan auri mata ba, sashinsu kuma ya ce: Ba zan ci nama ba, sashinsu ya ce: Ba zan yi bacci akan shinfiɗa ba, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi, sai ya ce: "Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai cewa ni ina sallah kuma ina bacci, ina azimi ina buɗe baki, kuma ina auren mata, wanda ya ƙi sunnata to ba ya tare da ni".
Explanation
Benefits
Sauƙin wannan shari'ar da rangwaminta, dan riƙo daga aikin Annabinta - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma shiriyarsa.
Alheri da albarka (suna) cikin koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da bin halayensa maɗaukaka.
Tsawatarwa daga tsanantawa kai a cikin ibadu da abinda ba zaka iya ba, kuma wannan yana daga halin 'yan bidi'a.
Ibnu Hajar ya ce: Riƙo da tsanantawa a cikin ibada yana kaiwa zuwa ƙosawa mai yanke asalin ibadar, kuma lazimtar taƙaituwa akan farillai misali, da barin nafilfili yana kaiwa zuwa fifita hutun sangarcewa, da rashin nishaɗi zuwa ga ibada, kuma mafificin al'amura tsaka-tsaki.
a cikinsa akwai bibiyar halayen manya dan yin koyi da ayyukansu, kuma cewa shi idan saninsa daga maza ya yi wahala to neman yayewarsa daga mata ya halatta.
A cikinsa akwai wa'azi da jefa mas'alolin ilimi da bayanin hukunce-hukunce ga mukallafai, da kawar da shubuha daga masu ijtihadi.
Umarni da sauƙaƙawa a cikin ibada, tare da kiyayewa a kanta da kuma farillai da nafilfili; dan musulmi ya kiyaye haƙƙoƙin waninsa a kansa.
a cikin hadisin akwai nuni akan falalar aure da kwaɗaitarwa a cikinsa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

