Rantsuwa mai sa anfani ce a haja (kayan sayarwa), kuma mai shafe albarkar riba ce
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Rantsuwa mai sa anfani ce a haja (kayan sayarwa), kuma mai shafe albarkar riba ce".
Explanation
Benefits
Kasuwanci na haram koda girmansa ya yawaita; to shi abin cirewa albarka ne babu alheri a cikinsa.
AlƘari ya ce: Tafiyar albarkar abin kasuwanci; kodai dan lalacewa ne wanda zai riske shi a cikin dukiyarsa, ko dan ciyar da shi a abinda anfaninsa ba zai koma zuwa gare shi ba a nan duniya ko ladansa a nan gaba (lahira), ko ya wanzu a wurinsa kuma a haramta masa anfaninsa, ko wanda ba zai gode masa ba ya gaje Shi.
Annawawi ya ce: A cikinsa akwai hani akan yawan rantsuwa a cikin ciniki, domin rantsuwa ba tare da wata buƙata ba abin ƙi ce, kuma zai haɗa da yawaitar haja gare shi, wataƙila mai siye ya ruɗu da rantsuwar.
Yawan rantsuwa tawaya ne a imani, kuma tawaya ne a cikin Tauhidi; domin cewa yawan rantsuwa yana kaiwa zuwa abubuwa biyu: Na farkonsu: Sakaci a cikin hakan da rashin kulawa, al'amari na biyu: Ƙarya, domin cewa duk wanda rantsuwarsa ta yawaita zai afka cikin ƙarya, to ƙaranta hakan yana kamata da kuma rashin yawaita rantsuwa, saboda haka ne tsarki ya tabbatar maSa Ya ce: {Ku kiyaye rantse-rantsenku} [al-Ma'idah: 89].
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

